Labarai

Fusataccen mutumin da yaje chakumar Buhari, gaisawa yake so yiyi dashi – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta bakin mai taimakawa shugaban Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa mutumin da yayi kokarin chakumar shugaban kasa Buhari a bikini shekarar da aka Saba yi a Argungun jihar Kebbi yayi kokarin ganin saiya gaisa da Buharin ne.

Majiyar DABO FM ta bayyana Femin yayi wannan batu ne a shafin sa na Twitter, inda yake karyata wadanda ke siyasantar da abin.

Bidiyon fusataccen matashin ya bayyana ne a kafafen Sada zumunta, cikin Bidiyon dai ana iya ganin matashin ya zaburo domin chakumar shugaban kasa inda kafin yakai daf dashi jami’an tsaro suka tare shi.

UA-131299779-2