Labarai

Kotu zata iya dawo min da sarauta ta, amma zan bude sabon babin rayuwa – Sarkin Kano ‘Murabus’

Sarkin Kano mai murabus, Mallam Muhammadu Sunusi II ya bayyana cewa da zai kai kara zuwa kotu, to lallai zai sam,u nasara kamar yadda Kotu ta umarta da a barshi yaje duk inda yake son zuwa yayi rayuwarshi.

DABO FM ta tattara cewar a jiya Juma’a ne wata babbar kotun tarayyar dake Abuja ta bayar da umarnin a kyale Sarkin Kano Sunusi mai murabus ya tafi duk inda yake so maimakon garin Awe na jihar Nassarawa da gwamnatin Kano ta korashi zuwa can.

A wani faifan bidiyo da DABO FM ta ganewa idanunta, an hangi Sarki Sunusi ‘Murabus’ yana bayyana yadda yake ji bayan ya rasa mulkin masarautar Kano dake da dumbin tarihi a masarautun duniya.

Muhammadu Sunusi yace tsigeshin da akayi ba bisa ka’ida bane, har ma yace ya tabbata kotu zata iya mayar da shi Sarki kamar yadda tayi umarni a barshi ya zauna duk inda yake so.

“Eh nasan akwai tsananin wuya amma ni a waje na ba wani abu bane.”

“Idan kuka duba dalilan da suka bayar na cire ni.

“Maganar gaskiya itace idan da inason komawa (Sarki)… abu ne mafi sauki inje Kotu.”

“Nayi abinda zanyi a cikin shekaru 6 da Allah Ya bani damar yi. Banason komawa, zan bude sabon shafin rayuwata.”

UA-131299779-2