//
Saturday, April 4

Neman Taimako: Kujerar gwamnan da ka hau ta gidanku ce? – Sheikh Jingir ga Masari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban kungiyar Izala Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya mayar da martani ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari akan wani furuci da akace gwamnan yayi.

DABO FM ta tattara cewar wasu rahotannin da basu da tabbci ba sun bayyana gwamna Masari yana korafi kan cewar kungiyoyin Izala da Darika sun cika masa ofishi da takardun neman taimako.

A wani faifan bidiyo da DABO FM ta samu, malamin ya bayyana fushinsa bisa ga kalaman gwamnan tare da kiranshi ‘dan Shi’a.’

Sai dai malamin ya tabbatar da bai ji maganar da gwamnan yayi ba, shi ma dai ji yayi “wai ance gwamnan yace.”

Masu Alaƙa  Bayan maganganu da tuhumar mantawa da talaka, a karshe, Dr Pantami ya fashe da Kuka

“Wani mugun gwamna wai a arewacin najeriya, wai sai yaje ya samu wasu yan tsalle tsalle suna kiran kansu yan izala, sai yace musu kun cika fitina kuna rubuto wasiku. Wai yana da wasika guda 20 daga yan izala dayan darika, wai fa bani naji ba.”

“Ya zamu zabi mutune da kuri’armu, ba’a bamu hakkinmu ba har dan rashin kunya mutun ya fito duniya yace wai ‘yan Izala da Darika suna cewa gwamnati ta taimaka musu, gwamnatin taka ce? ka hau daga gidan babanka ne?

Kalli cikakken bidiyon anan:

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020