Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Fusatattun Mutane sun afkawa sakatariyar APC, sun sace Talbijin da Kujeru

2 min read

Wasu da ba san ko su wane ba, sun barke sakareriyar jam’iyyar APC ta jihar Ogun, su ka sace takardun muhimman bayanai tare da sace kayayyakin da ke cikin sakateriyar.

Wasu mutane da ba’a san ko suwaye su ba, sun afkawa babban ofishin jami’iyyar APC na jihar Ogun, suka samu nasarar yin awon gaba da wasu takardu masu dauke da muhimman bayanai da kayayyakin masu amfani.

Sashin Hausa na JAridar Premium Times ta rawaito cewa; mutanen basu tsaya iya nan ba, sai da ta kai sun lalata wasu sassan sakatariyar tare da yin ta’annati ga rufin silin ofisoshin dake cikin sakatariyar.

Majiyoyin DaboFM sun rawaito daga Times cewa, kayayyakin da mutanen suka sace sun hada da, Takardu, Na’urar Sanyaya waje ‘A.C’, Talbijin dake dukkanin ofishin hadi da Kujeru.

Deri Adebiyi, shugaban jami’iyyar APC na jihar ya sanar da al’amarin a wani taron manema labarai da yayi a babban birnin jihar Ogun.

Ya bada sanarwar cewa an fasa ofishin ne da tsakar daren Larabar data gabata.

Cikin ofishin da abin ya faru ya hada dana sakataren jami’iyyar da sakataren gudanarwar jami’iyyar ta jihar Ogun.

Ya bayyana cewa fasa ofishin bazai rasa nasaba da wata makarkashiya da ake shiryawa ba, duba da kwanakin da suke da kasa da makonni biyu kafin wa’adin gwamnan jihar Amosun ya kare.

Haka zakila dai tini yace sun sanarwa da yan sanda faruwar lamarin kuma yayi kira ga mutane dasu kwantar da hankalinsu.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.