Labarai

Fusatattun ‘Yan Najeriya sun kai wa Ministan Sufurin Najeriya hari a kasar Andalus

Ministan sufuri na Najeriya Mr. Rotimi Amaechi ya bayyana cewar wasu marasa tarbiyya sun Kai masa hari a lokacin da ya halarci taro a birnin Madrid na kasar Andalus (Spain).

A cewarsa, ta shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa wasu bata garin ‘yan Najeriya marasa tarbiyya sun kai masa hari yayin gudanar da taron chanjin yanayi a birnin Madrid na kasar Andalus.

Ministan yace cikin gaggawa jami’an ‘yan sanda sun yi kokarin tarwatsasu.

Ya kuma bayyana cewa yana yan cikin koshin lafiya, akan haka ya kara yin godiya a bisa addu’ar da ake yi masa ta masoya.

Taron dai da majalissar dinkin duniya ta shirya a wannan shekara ta 2019, wanda ake wa taken COP25, shine taro na ashirin da biyar da yake tattaunawa akan sauyin yanayi da dumamarsa a duniya.

Karin Labarai

UA-131299779-2