Labarai

Wasu mutane sun siyar da Matan Pakistan kimanin 600 zuwa kasar Sin

Wani binciken da aka gudanar, ya bayyana cewar a cikin kasa da shekaru biyu kawai, an yi cinikin wasu mata da suka kai dari shida da ashirin da tara zuwa kasar Sin daga Pakistan.

Wannan dai lamari shine mafi girma da girgiza hukuma bayan rahoton ya shiga hannun hukuma.

Da yawa daga cikin wadanda wannan ciniki ya rutsa da su, saboda fargaba da zullumin da suke ciki, sun kasa bayyana yanda wannan balahira ta samesu. Domin sun kasa cewa uffan.

Wani jami’i a hukumar kula da fasa-kwaurin mutane a kasar Pakistan Mr. Sadiq, ya bayar da tabbacin za a yi kokarin mayar da su asalin yankunansu. Duk da cewar kawo yanzu bai bayar da cikakken bayanin wadanda suka kubuta ba.

Kasar Pakistan da kuma makociyarta India sun jima suna fama da wannan matsala ta safara mutane, kususan mata, wanda akan tsallaka da su don yin aikatau, wasu kuma karuwanci don samar da kudi ga wadanda suke kula da su.

Karin Labarai

UA-131299779-2