Labarai

Rikicin Fulani yayi sanadiyyar rasa rai a jihar Jigawa

A yammacin Daren jiya Alhamis, da misalin karfe 8:00 na dare, an samu hatsaniya tsakanin Fulani da Makiyaya a kauyen Bodala dake kan hanyar Adiyani a karamar Hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda ta jihar Jigawa SP Abdul Jinjiri ya tabbatarwa da wakikin DABO FM faruwar al’marin bayan tattauanawarsu ta wayar tarho.

Cikin hirar a wayar tarho da sanyin safiyar yau, SP Jinjiri ya tabbatar da aukuwar hakan, ya kuma tabbatar da mutuwar mutum guda.

Ya bayyana wanda ya rasa ranshi da sunan Abubakar Dauda, mai shekaru 38.

DABO FM ta tabbatar da cewa ; Abubakar Dauda, ya gamu da ajalinsa ne sakamakon sassara shi da Fulanin sukayi, a inda ya rasa ranshi bayan an kaishi babban asibitin kwanciya na garin Guri.

SP Abdul ya tabbatar da kama mutum guda, tare da tabbatar da cewa; “Bisa umarnin Kwamishinan yan sanda na jihar Jigawa, an tura jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya faru don gujewar tashin hankali.

Kawo Yanzu dai Gwamnatin jihar bata ce komai game da batun ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan bindiga sun hallaka mutane a jihar Jigawa

Dabo Online

Kungiyar mata ‘yan asalin jihar Jigawa sun fara aikin bada magani kyauta a fadin jihar

Rilwanu A. Shehu

Gwamna Badaru ya amince da gabatar da Sallar Idi a jihar Jigawa, ya gindaya sharuda

Dabo Online

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisa a Jigawa

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin jihar Jigawa zata fara biyan albashin N30,000 a watan Disamba

Hassan M. Ringim

An kashe Manomi sakamakon rikicin Fulani a jihar Jigawa

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2