Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnatin sa na tsammanin yawan talakawan Najeriya zai ninka har sau uku dalilin annobar Kwaronabairas.
Rahoton DABO FM ya bayyana mai magana da yawun shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar.
Femi ya bayyana shugaba Buhari ya fadi hakan cikin wani taron yanar gizo da aka gudanar na majalisar dinkin duniya na dabarun kakkabe bakin talauci a fadin duniya baki daya.
Cikin wani rahoton bincike da aka fitar a shekarar 2019 dai ya bayya fiye da mutum miliyan 82.9 ke fama da talauci a fadin Najeriya. Da yake nuna damuwar sa kan mutanen dake cikin wannan hali na talauci, Buhari ya bayyana a fadin duniya kashi goma wato kusan mutane milyan 700 na cikin bakin talauci.
“Muna da yawan mutane da suka doshi miliyan 200, kaso mafi yawa na cikin uzuwa daban daban na talauci, sun hada da na rashin abin hannu, rashin abinci mai gina jiki, rashin wajen zama, lafiya, ilimi da ruwa mai tsafta.”
“Tilas cikin wannan hali kuwa a tsammaci ninkawar masu fama da talauci zuwa ninki 3.”
