Home LabaraiƘurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

Ƙurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin cewa kada kowani minista da ya tafi kasar waje sama da sau biyu a kwatan zango.

Ministoci za su iya fita wajen kasar ne sau takwas kacal a shekara, ministan labarai, al’adu da yawon bude ido, Lai Mohammed ya bayyana. Kamar jaridar Legit ta ruwaito.

Bayan nan, kada kowani minista dake ziyarar aiki a kasar waje ya tafi da hadimai wadanda ke da muhimmanci a tafiyar sama da guda hudu.

Daga yanzu jami’an gwamnatin tarayya da ke kasa da mukamin ministoci za su kasance da hadimai kadan. Sannan daga yanzu ba za a dunga lissafin kudin tafiya a kan kowani sa’a ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00