Ganduje ya soke yin ‘Hawan Nassarawa’ da masarautar Kano takeyi duk ranar 3 ga Sallah

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya soke gudanar da bikin hawan Nassarawa da masarautar Kano ta sabayi dukkanin kwanaki 3 bayan kowanne bikin Sallah.

DaboFM ta rawaito mai yada labaran gwamnatin jihar, Anwar , yace gwamna GAnduje ya soke yin hawan ne bisa wasu dalilan tsaro.

“Bayan ganawa da Ganduje yayi da jami’an tsaro kamar yadda aka sabayi a duk shekarar, an samu rahoto cewa akwai matsala daka iya kawowa zaman lafiya cikas.”

“Saboda dalilin rahotan da aka samu yayin ganawa da jami’an tsaro, gwamnatin jihar Kano ta soke hawan Nassarawa da masarautar Kano zatayi ranar 3 ga Sallah.”

“Tini dai gwamnatin jihar Kano ta sanar da masarautar Kano, bisa matsayarta na dakatar da hawan a cikin gari.”

%d bloggers like this: