Yarda da Allah ce ta sanya nake murmushi ko ina cikin damuwa – Mesut Ozil

Tsohon dan wasan kwallon kafa ta kasar Germany, Mesut Ozil ya bayyana yardar a matsayin garkuwa da take taimakonshi a rayuwa.

Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafukanshi na sada zumunta.

Ozil yace; “Yarda da Allah ce tasa nake murmushi ko ina cikin damuwa, idan na shiga cikin rikici, nake fahimta na kuma gane.

“Yarda da Allah ce take sawa ko da za’a daureni, nake yarda da mutum.”

DABO FM ta tattara cewar makonni da suka gabata, Mesut Ozil yayi kalaman suka ga kasar China akan zargin da akeyi wa kasar na azabtar da Musulman kabilar Uyghurs dake rayuwa a lardin Xinjiang na kasar China.

Lamarin da ya janyo aka cire hotuna da bidiyon dan wasan a cikin wasannin kallo na kwallon kafa da ake bugawa a kasar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.