Tsohon kakakin majalissar wakilan Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na’abba, ya na nan da rai cikin koshin lafiya, DABO FM tana da tabbaci.
Rahotanni da dama a kafafen sada zumunta da ciki har da rahoton wata babbar jarida sun bayyana mutuwar tsohon kakakin majalissar da yayi zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo.
Wasu daga cikin rahotannin sun alakanta ‘mutuwar’ sakamakon cutar nan ta Kwabid-19 da ta addabi duniya.
DABO FM ta tuntubi iyalan Alhaji Ghali Na’abba akan batun, sun kuma tabbatar mana da cewa yana cikin koshin lafiya a can birnin Landan dake kasar Burtaniya.
An dai haifeshi a shekarar 1958 a garin Kano, ya kasance dan jami’iyyar PDP a wancen lokaci. Sai dai a watan Maris na shekarar 2015, Ghali Na’abba ya koma jami’iyyar APC a karkashin shugabancin John Onyegu kwanaki kadan kafin a kada kuri’a a babban zaben 2015.
