Labarai

Yawancin wadanda ake hada karya a kansu, su na kare wa su shiga cikin aljanna – Ghali Na’abba

Rt Hon Ghali Umar Na’abba ya bayyana cewa yawanci wadanda ake hada jita-jita a kansu suna mutuwa ne su shiga al’janna.

Ghali ya bayyana haka ne yayin wata ganawarshi da Dele Momodu a hirar kai tsaye ta shafin Instagram.

A safiyar yau ne dai akayi ta yada jita-jitar mutuwar tsohon kakakin na majalissar Najeriya, Hon Ghali Umar Na’abba a kafofin sadarwa da wasu manyan jaridu irinsu The Sun da kuma Sahara Reporters.

DABO FM ta tattara cewar kafin hirar, Dele Momodu ya ayyana cewar zai aiye tarihi domin zai yi hira da matattace, da nufin nuna wa duniya cewar Hon Ghali yana cikin koshin lafiya.

Ga yadda hirar ta kasance;

Dele: “Yau zan ajiye tarihi, zan yi magana da wanda ya riga ya mutu.”

Na’abba: (Dariya)

Dele: Ya ya aljanna, na san kana can.

Ghali: Ba zan ce komai a kai ba tinda ban shiga ba. Amma yawanci wadanda ake hada labarun karya a kansu, su na kare wa kuma su shiga cikin aljannar.

A cikin hirar ya bayyana cewar yana cikin koshin lafiya, babu abinda yake damunshi har ma ya ce rufe iyakoki da akayi ne ya hana shi dawowa gida Najeriya.

Da yake tsokaci kan mace-macen da akeyi a Kano, Ghali ya alakanta yawan mace-macen da talauci da mutane suke fama dashi.

Karin Labarai

UA-131299779-2