0
‘Yar gidan Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ta samu maki mafi daraja a digirin data kammala.
Dabo FM ta samo rahoton daga bakin mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari wanda ta wallafa a shafukan ta na sadarwa.
Aisha Buhari tace “Alhamdulillah a yau mun taru tare da ‘yan uwa da abokan arziki domin taya ‘ya ta Aisha Muhammad Buhari karama wato Hanan murnar kammala digiri da mataki mafi daraja.”
“Ina kuma godiya ga mutanen arziki dake jihar Kebbi domin kulawa da ta samu yayin da take aikin kammala digirin ta.”
“Musamman Gwamna Atiku Bagudu, Ibrahim Bagudu, Matar Gwamna, Sarkin Gwandu da Sarkin Daura.”
