Labarai

Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta kaddamar da shirin ciyarwar azumi kyauta

Gidauniyar Hadeeyatul Khair dake jihar Kano ta kaddamar da shiri na farko da zata fara yi na ciyar da marasa karfi a lokacin azumin Ramadan.

Gidauniyar tace zata rika rarraba kayyakin abinci zuwa ga gidajen mabukata dake birnin Kano da kewaye.

A wata sanarwar da shugabar gidauniyar Dr Mufidah Ibrahim Fari ta aikewa DABO FM tace tsarin ya kunshi ciyar da kafatanin gidajen masu iyali har na tsawo watan daya tin daga farawar azumi har gamawa.

Haka zalika tace gidaniyar zata raba danyen abinci da dafaffe da kuma ruwan sha.

Dr Mufida tayi kira ga masu son bayar da tallafin kayan abinci ga kungiyar domin aiwatar da shirin zasu iya taimakawa ta hanyar tuntubar gidauniyar a ofishinta dake unguwar Kabuga dake jihar Kano.

“Ga masu bukatar bayar da tallafin kudi, mun kiyasta kashe N30,000 ga gidajen da suke da babban iyali, N15,000 a gidajen da suke da karamin iyali.”

Tace akwai shirin ciyarwar mako wanda suka kiyasta kashe 3,500 ga kowanne gida karamin mai iyali.

Ga masu son taimakawa zasu iya tuntubarsu a ofishinsu dake Kabuga a jihar Kano ko a nemesu ta lambobin +2347068255776 ko +2348030609682.

Ga masu bukatar sanya kudadensu na taimako;

Heritage Bank

1907365785

Fatima Ibrahim Fari

Karin Labarai

Masu Alaka

Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta fara koyar da Sana’o’i da darussan ilimin a yanar gizo

Faiza
UA-131299779-2