Sadiya Umar Faruk
Labarai

Mun fara rabawa marasa karfi kudi – Minsita

Ministar ayyukan agaji da bala’i, Sadiya Umar Farouk tace tini gwamnati tarayya ta fara rabawa marasa karfi kudade domin rage radadin takaita fita.

Ministar ta bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a babban birnin tarayyar na Abuja.

Duk da ministar ba ta ayyana adadin kudaden ba, tace dai tini aka fara turawa marasa karfi kudaden da hanyar banki domin ya zama kamar tallafi biyo bayan dokar zaman gida da gwamnati ta fitar.

Tace; “A jawabin shugaban kasa, saki layi na 54, ya bayar da umarnin tura kudade da zasu ishi mutane na tsawon watanni biyu.”

“Tini mun bayar da umarnin turawa marasa karfi da masu neman dauki a kasa baki daya.”

“Saboda wannan annobar ta Coronavirus, masu tsananin bukata zasu karu saboda muna sane cewa mutane dayawa suna rayuwa kan abinda suke samu a kullin, fon haka zamu duka wadannan mutane domin ganin yadda zamu basu abinci a wannan lokacin da ake ciki.”

Karin Labarai

UA-131299779-2