Rahotanni sun bayyana yadda wasu matasa a unguwar Dabai dake karamar hukumar Dala ta jihar Kano suka rushe gidan wanda ake zargi da yin batanci ga shugaba Sallalahu Alaihi Wasallam.
Kamar yadda DABO FM ta shaidawa idanuwanta a ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare bayan kai ziyara wajen da abin ya faru, mun tabbatar da rushen gidan.
Tin a Asabar munyi kokarin jin ta bakin mahukuntan unguwar, sai dai sun bukaci da mu dawo yau Lahadi domin jin karin bayani daga wajensu.
A dai dai karfe 11:20 na safiyar Lahadi, yayin da muke tattaunawa da mai Dagacin unguwar Dabai, Malam Sunusi Yallabai, aka kawo masa rahotan yadda wasu mutane sukazo a motoci guda 2 da babura masu tarin yawa.
An tabbatarwa da mai unguwar cewa “sunzo ne domin su dau fansar rushe gidan da akayi wa dan uwansu.”
Sai dai ko da yake akwai tafiya tsakanin fadar mai unguwa da gidan mutumin da aka rushe, kafin zuwanmu wajen, sun tattara nasu sun tsere.
Wasu shaidun ido da muka samu sun bayana mana cewar mutanen sunzo ne domin su tayar musu da hankali, suna zikiri, sunata zage-zage.
“Sun taho suna Zikiri, suna ta zage-zage, tin jiya muke ta wannan rigimar kokarin kwantar da tarzoma, su kuma sunzo suna ta kokarin su kuma tayar mana da rigima.”
“Sun zo a mota guda biyu da babura masu yawa sosai, sunzo mana tashin hankali, suna neman su sa mutanen gari su biye musu ayi rigima.”
“Motocin kirar Honda Odyssey da Honda Panadol Extra da baburan Roba-Roba da Karfe-Karfe.”
Sai dai sun bayyana mana cewar mutanen dake wajen sun yi kokarin korarsu tare da tsoran da sukaji na cewar jami’an yan sanda suna kan hanyarsu ta zuwa, kamar yadda zaku gani a bidiyon kasa.
DABO FM ta kuma tattaunawa da shugaban yan kwamitin Dabai da Goron Dutse, unguwar Dabai, Babalili Abdullahi domin jin yadda al’amarin ya kasance.
Ya bayyana cewar yayi kokari wajen kiran jami’an tsaro da ‘yan kwamatin unguwar fiya da mambobi sama da 100 da mai unguwa domin su kawo dauki tare da dakile matsalolin da suka taso.
Babalili ya kara da cewa “Yan sanda sunyi iya kokarin su wajen kare iyalan wanda ake zargi, duk da kukarin ma’aikatan tsaron sai da aka sawa makotan wuta da harda yaron daya karye Wanda baiji ba Bai gani ba.
Da muka tambayi shugaban kwamitin ko ina wannan Wanda yayi batanci da Annabi take? Shin ya Shiga hannu ko kuwa? Babalili ya tabbatar mana da cewa tun kafin su iso wajen ya tsere, don haka suna nan suna farautar sa domin gurfanar dashi gaban Shari’a.
Da muka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa, yace al’amarin bai iso gareshi ba, sai dai yace zai sanar damu da zarar ya samu labarin.
