Gidauniyar Kwankwasiyya zata daukin nauyin Dalibai domin yin Digiri na biyu a kasashen waje

Gidauniyar Ilimi ta Kwankwasiyya na neman dalibai dasuka kammala Digiri na farko domin turasu yin digiri na biyu  a kasashen waje.

A cigaba da shirin da gidauniyar takeyi na bunkusa Ilimi, gidauniyar ta shirya wajen daukar nauyin karatun Dalibai domin karo karatu a kasar waje.

Daliban da suka gama Digiri na farko kuma ‘yan kasa da shekara 30 ne zasu amfana da wannan shiri.

An bukaci duk mai sha’awar morar shirin daya mika takardunshi zuwa ga Gidan Kwankwasiyya dake kan titin Lugard, Bompai GRA a cikin birnin Kano.

Sanarwar tace daga yau Juma’a 12 ga watan Afirilun 2019, gidauniyar zata fara karbar takardun dalibai har zuwa sati biyu nan gaba.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Wani matashin Kwankwasiyya yayi barazanar zama dan kungiyar Boko Haram idan ba'ayi musu adalci a zaben gwamnan Kano ba

Daliban zasu je gurin mika takardun da shaidar kammala Digiri na farko, Takardar haihuwa, da duk wata takardar daka iya taimakawa.

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.