Kasar Isra’ila ta mayar da wani babban masallaci gidan shan giya a kasar

Kasar Isra’ila ta mayar da wani masallaci mai tarihi a kasar gidan rawa da shan giya.

Hukumar unguwar  Safed ta mayar da masallacin AL-Ahmar zuwa dakin taro, kulub din rawa da kuma wajen shan giya.

Masallacin Al-Ahmar dai na daya daga cikin manyan masallatai masu tarihi a daular musulunci.

Wannan ba shine karon farko da hukumomin kasar suke maida masallacin wani abu da suke so ba. Tin bayan da Yahudawan suka kwace masallacin a shekarar 1948, sunyi ta sauyawa masallacin fasali.

A shekarun baya, sun taba maida masallacin wajen yin takuran siyasa, wajen koyar da Yahudanci inda daga karshe dai suka maida wajen gurin ajiya da siyar da kayan sawa.

Jaridun kasar Ingila sun rawaito cewa, yanzu dai masallacin yana matsayin gurin shakatawa inda ya koma kulub din rawa tare da dakunan shan giya a ciki.

Hukumomin garin sun chanzawa masallacin suna daga “Masallacin Al-Ahmar zuwa Khan Al-Ahmar.

Wata kungiyar musulmin unguwar Safed ta shigar da kara tare da nuna takardun mallakar masallacin da musulman suke dashi.

Rahotanni sun nuna cewa bisa sahalewar hukumar unguwar Safed, za’a iya yin komai a cikin masallacin amma banda Sallar musulmai.

%d bloggers like this: