Gidauniyar NURU zata dauki nauyin karatun Marayu na tsawon shekaru 5

Gidauniyar Nuru, tana son sanar da al’umma cewa zata fara kai ziyara zuwa Gidan Marayu dake garin Zariya ta jihar Kaduna da kuma sansanin ‘yan gudun Hijira na garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Za’a gudanar da ziyarar , a garuruwan Abuja da Kaduna.

Gidauniyar ta shirya ziyarar ne domin kai kayayyakin tallafi zuwa ga Marayu da ‘yan Gudun Hijira, wanda yin hakan yana daga cikin makasudin kirkirar gidauniyar.

Ga masu neman Tallafin Karatu, su da kansu, ko wakilansu, zasu iya neman tallafin kai tsaye da shafinsu na yanar gizo-gizo. –Zamu saka shi a kasa.

Haka zalika, gidauniyar ta bude shirin daukar nauyin karatun Yara daga ajin JSS 1 zuwa SS2.

Ga wasu daga cikin kudurorin gidauniyar Nuru;

  • Ciyar da mabukata a lokacin azumin watan Ramadana.
  • Rarraba kayayyakin sawa.
  • Tallafin kudi domin karatun Marayu.
  • Samar da tsaftaccen Ruwan Sha.
  • Daukar Nauyin Karatun Marayu.
  • Wayar da kai akan illolin shaye-shayen kwayoyi da cin mutunci Mata.
  • Samarwa Mata Ilimi.
  • Shirya tarukan wayar da kawuna.
  • Samar da makarantun Islamiyya.
  • Shirin Inganta lafiya a kauyuka.

Gidauniyar ta bayyanawa Dabo FM cewa; ga masu son hada hannu wajen tallafawa gidauniyar, zasu iya yin rijista akan shafinta na yanar Gizo-gizo, wanda zaku gani a nan kasa.

http://www.nurugroup.org

Ta kara da cewa; “Ga masu son bayar da kyautar kayan sakawa, zasu iya tuntubar wakilansu kamar haka;

Abdulbasit Suleiman (Zariya) 07039601525                         

Ahmad Abubakar (Zariya) 09061650646

Suleiman Tahir ( Abuja )         08102628353

Abdullahi Barau ( Abuja ) 08112495578

Abdulrahman Barau ( Abuja ) 08058878723

Whatapp: https://wa.me/2348141540744

Instagram: https://instagram.com/nuru_foundation

Facebook: https://www.facebook.com/Nurufoundation/

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.