Siyasa

Dawafin 7 sau 7 muka yiwa Ganduje kafin ya iya cire Jar Hula saboda kulle-kullen cikinta – Ali Baba

Alibaba Agama lafiya

Tsohon mai bawa gwamnan jihar Kano shawara akan sha’anin addinin, Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge, ya bayyana irin tsananin wuyar da suka sha kafin gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje, ya cire Jar Hula.

Dabo FM ta tattaro daga wata hirar da Ali Baba yayi da gidan Rediyon Express dake Kano tare da Salamatu Sabo Bakin-Zuwo.

Hirar da yayi ta nuna farinciki da hukunci Kotun korafe-korafen zabe na tabbatar da nasarar Dr Ganduje, Ali Baba ya bayyana Jar Hula a matsayin wani siddabaru da Kwankwaso yake yiwa masu sanya ta.

“Cire Jar Hula ba abune mai sauki ba, muma sai da mukayi ta yin Laqad Ja Akum, Li’ilafi, Ayatul Kurisiyyu”

“Wallahi wannan Jar hular daka ganta, kafin ya cire ta (Ganduje), sai da mukayi ta dawafi.”

“Kowa ya cire Jar Hula, sai Ganduje, in zai shiga wanka ma da Jar Hula, ko ina shiga yake da ita sai dai wajen dawafi ne kawai yake cirewa.”

“Daga nan fa mukace wannan Jar Hular ta kan Ganduje tafi kama kansa, anfi kaita wajen mutanen nashi (Indiya), shine muka zuba mata dawafin 7 sau 7.”