Labarai

Gidauniyar Taufeeq ta duba marasa lafiya da bada magani kyauta a Zariya

A kokarin ta na inganta lafiyar al’umma a matakin yankunan karkar, Gidauniyar kula da lafiya ta Taufeeq da ke Zariya a Jihar Kaduna, ta gabatar da taron wayar da kan Jama’a game da kiwon lafiyar su da kuma dubawa tare da bada magani har ma da shawar-wari kyauta, akan cututtukan da suke damun al’umma na yau da kullum.

Taron, wanda aka gudanar a yankin Aba dake cikin karamar hukumar Zariya, ya samu halartan shuwagabannin al’umma da mutanen gari.

Da yake jawabi wurin kaddamar da bada maganin, hakimin Birnin Zariya da kewaye kuma Sarkin Kudun Zazzau Barista Muhammad Sambo Shehu Idris, wanda shugaban kwamitin kula da lafiya na ofishin hakimin birnin da kewaye kuma Mardannin Zazzau Alhaji Lawal Ahmad Rufa’i ya wakilta, ya ce, aikin taimakon al’umma a bangaren kiwon lafiyar, abu ne mai matukar muhinmanci da ya kamata a ce kowwane dan kasa ya himmatu wurin aiwatar da shi.

Kuma ya tabbatar da kudirin ofishin hakimin birnin da kewaye wurin aiki da kungiyoyi irin wannan kasancewar suna da manufa mai matukar muhinmanci.

Ya sanyawa gidauniyar Albarka, kuma ya bukaci su kara ninkawa akan kokarin da su ke yanzu haka, sannan ya shawarci wanda za su amfana da gajiyar, su yi amfani da shi kamar yadda ya dace.

Da ya juya ga al’umma kuwa, shawartan su ya yi su dauki ragamar taimakon al’umma domin rage ma gwamnati wani nauyin da ya rataya a kanta.

Da yake nashi jawabin, shugaban Gidauniyar ta Taupeeq Dakta Nuraddin Umar, ya ce, an kafa Gidauniyar ce tun shekaru 8 da suka gabata. Kuma manufar kafa ta shi ne taimakon al’umma a bangaren kiwon lafiya da horas da matasa masu tasowa a kan abun da ya shafi aikin likitanci harma da taimakon gajiyayyu da marasa galihu cikin al’umma.

Kuma tun bayan kafa ta zuwa yau, an samu gagarumar nasara musamman a bangaren taimakon al’umma bangaren kiwon lafiya.

A cewar Dakta Nuraddin, dukkanin abubuwan da suke gudanarwa a gidauniyar, taimako ce da ake samu daga membobin kungiyar, domin kawo yanzu basa samun wani agaji ko taimakon daga wani zababbe ko wasu dai-daikun al’umma.

Sannan ya tabbatar da cewar, Shirin na su na bada magunguna kyauta ga al’ummar Aba, ba shi ne karo na farko ba, Sai dai a wannan karon kadai ana sa ran mutane akalla 500 za su amfana.

Da yake nashi jawabin, daya daga cikin jagororin Gidauniyar Dakta Ibrahim Muhammad Waziri, ya yi bayani ne akan sabuwar cutar nan da ta shigo Najeriya mai sarke numfashi wato COVIC19 da cutar Zazzabin Lassa, kuma ya yi bita akan alamomin cutar da hanyoyin kariya daga daga cutar.
Ya shawarci al’umma su rika gaggawar zuwa asibitocin kula da lafiya a matakin farko da zarar anga alamar mutum ya kamu da wata cutar da ba a gane ta ba.

A jawaban su daban-daban, Sarkin Aba Malam Abdurahman Yusuf da na Nagoyi Malam Yusuf Jafaru Isiyaku, sun nuna matukar farin cikin su ne tare da godiya ga Gidauniyar bisa namijin kokarin da suka yi suka kai tallafin a yankin na Aba, kuma sun naimi ganin hukumomi a kowanne mataki, suna taimakawa irin wadannan kungiyoyin da ke da manufar inganta rayuwar al’umma a yankunan karkar.

A karshen taron dai, an bada takardar izinin shiga makarantar guda 10 da dubawa tare da bada magunguna kyauta a yankin.

Wasu daga cikin al’ummar da suka ci gajiyar wannan shiri, sun gode ma karamcin da Gidauniyar ta Taufeeq ta yi masu ne, kuma suka yi addu’an Allah ya saka masu da mafificin alherin sa.

UA-131299779-2