Tsohon sanatan Kaduna, Kwamared Shehu Sani ya bayyana talakawa kada su kara yarda da duk wani dan takarar da zai zo yana wa talakawa yan koke-koke domin yaudare ce zallar ta.
Majiyar DABO FM ta bayyana Sanatan yayi wannan furici ne a fejikan sa na sada zumanta a yammacin ranar Juma’a.
Shehu Sani yace “Daga yanzu duk dan takarar shugaban kasar da ya sake zuwa muku dauke da farin hankici yana koke-koke to kuyi ta kanku [domin zallar yaudara ce.”
Wannan yana zuwa ne bayan mawuyacin halin da yan kasar suka fada daga karbar mulkin shugaba Buhari, wanda a wannan takin shugaban kasa Buhari ke shan zazzafar adawa.
Next time when you see Presidential candidates shedding tears with handkerchief during campaigns,my people make una run🏃♂️