Labarai

Sarki Sunusi: Rikici ya barke a zauren Majalissar Kano kan tsige Sarki

Rahotani daga zauren Majalissar jihar Kano ya tabbatar da barkewar rikici yayin zaman zauren Majalissar a yau Litinin.

Wasu daga cikin yan majalissar sun hana zaman ne bayan gabatar da kudirin kan binciken mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II inda wasu daga ciki suka zargin kudirin da son tsige Sarkin.

A dai cikin makon nan dai wata Kotu a jihar Kano ta dakatar da hukumar karfe korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano daga binciken Sarki Muhammadu Sunusi II.

Rahotannin sun bayyana yadda wasu daga cikin yan Mjalissar wadandnda ake zargin na cikin garin Kano ne sukayi yunkurin dauke sandar Majalissar.

Zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, majalissar ta shiga zaman gaggawa domin shawo kan matsalar.

UA-131299779-2