Kano: CP Wakili ya kama ‘Yan fashi da masu dillancin Kwayoyi 142 a kwana 4

Karatun minti 1

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishinan Muhammad Wakili ta kama wadanda take zargi da aikata manyan laifukan da suka hada fashi da makami, dillancin kwayoyi da sauran manyan laifuka.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdullahi, ya bayyanawa manema labarai cewa rundunar ta kame mutane 142 daga ranar 29 ga watan Maris din 2019 zuwa 1 ga watan Afirilun 2019.

Wasu daga cikin masu laifin

Yace mutane da ake zargi da aikata laifukan duk sun amsa laifukansu, kuma zasuyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da sun mika su gaban kotu domin karbar hukunci dai dai yacce doka ta tanada.

“Dukkannin wadanda muka kama da laifukan sun amsa laifinsu.”

“Zamu cigaba da gudanar da aikin mu a jihar Kano har sai masu laifuka sun shiryu sun bari, ko kuma mukame domin mu kai su su fuskanci hukunci.

Daga cikin kayyakin da aka kama tare da masu laifin, akwai talabijin, munanan makamai da suka hadar da addina, wukake, barandamai.

Kayayyakin shaye-shaye sun hadar da tabar wiwi, madarar sikudayin, sholi-sho da sauran miyagun kwayoyi.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog