Home LabaraiGobara ta kone shaguna 39 a kasuwar ƴan katako dake Abuja

Gobara ta kone shaguna 39 a kasuwar ƴan katako dake Abuja

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Gobara ta tashi cikin dare tare da cinye kayan kudi na miliyoyin nairori a cikin shaguna 39 a kasuwar yan katako ta Kubgo dake babban birnin tarayyar Najeriya.

Rahoton Dabo FM ya tabbatar da gobarar ta tashi da misalin karfe 12 na daren ranar Litinin a kasuwar dake makwaftaka da Mogadishu Barracks da Nyanya.

Shugaban kasuwar, Austin Onuh wanda shima yana ciki wanda shagunan sa suka kone kurmus ya bayyana kiyasin kimanin naira miliyan 21 ne suka salwanta. Kamar yadda DailyTrust ta fitar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00