Gwamnatin Indiya ta bayar da hutun wasan ‘Jirgin Leda’

Hukumomin kasar Indiya sun bayar da hutu domin zagoyowar ranar da ake kiranta Uttarayan ko kuma Makar Sankrati, ranar ce da suke sadaukar da ita ga wani abun bautarsu mai suna Surya.

DABO FM ta tattara cewa ana murna da zagayowar ranar ne ta hanyar kada Jirgin Leda, wanda shuwagabanni da duk ‘yan kasa suke fitowa domin murnar ranar wacce take tilasta dakatar da dukkanin ayyukan ranar.

Ranar tana zuwa ne a duk 14 ga watan Janairun kowacce shekara.

Manufar murna da ranar Uttarayan shine domin yin murna da canjin waje da Rana ta samu daga inda take ta kuma nufi sashin rabin duniya na arewaci.

Masu Alaƙa  Jami'an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

Ana rufe duk makarantu, dayawa cikin ‘yan kasuwa basa fito wa cin kasuwanci, motocin zirga-zirga suna wahala duk dai a ranar.

Yayin zantawarmu da wani dalibi dan Najeriya dake zaune a kasar ta Indiya, ya shaida mana yadda ‘yan kasar musamman wadanda ba musulmai ba suke girmama ranar.

Yace; “Tabbas yau rana ce mai matukar muhimmanci a kasar Indiya, domin anan inda muke yau tituna gaba daya babu mutane, duk guraren da suke da cunkoso, yau babu kowa.”

“Amma Musulmai basa yi, sai dai suma dai sunce suna kada jirgin ne kawai domin nishadi ba don tinawa da ranar ba.

Daga shafukan shuwagannin kasar; Inda suke kada jirgin tare da mutanensu;

Masu Alaƙa  Indiya: An kama dan Najeriya da Hodar Iblis "Cocaine" a kasar Indiya

Farawa da Firaminista, Narendra Modi

Babban Ministan (Gwamna) jihar Rajasthan, Mista Ashok Gehlot

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.