Labarai

NBTE ta gamsu da yadda NubaPoly ke gudanar da harkokin karatu a makarantar

Shugaban sashin kula da kwalejojin Kimiyya da fasaha dama kere-kere ta hukumar kula da ingancin ilimi ta kasa shiyyar kaduna wato NBTE Alhaji Musa Muhammad Lagogo, ya bayyana Makarantar Kimiyya da fasa ta Nuhu Bamalli dake Zariya a matsayin wacce ta samu nasara a wasu daga cikin fannonin da take koyar da dalibai a kwasa-kwsai daban-daban tun lokacin da aka kafa ta zuwa yau.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai, Jim bakadan bayan shi da tawagarsa sun gama bankwana da majalisar zartaswar Makarantar, bayan da ya jagoranci tawagar kwararru da suka zo domin duba yanda Makarantar ke gudanar da harkokin karatun ta da kuma daga darajar wasu daga cikin kwasa-kwasan da ake koyarwa yanzu haka.

Ya ce, ya gamsu matuka da yadda Makarantar ta dukufa wurin gudanar da harkokin ta, duk da cewa akwai wasu fannoni da ya kamata a sake zage damtse kuma a kara kaimi a kai.

Ya kara da cewa, duk da ba yanzu ne kwamitin nasa zai bayyana sakamakon karshe na binciken da suka yi ba, amma abun da suka gani da idanuwar su ya nuna ana samun cigaba a harkokin koyo da koyarwa a Makarantar.

Sai dai ya shawarci gwamnatin Jihar Kaduna ta kara inganta albashin malaman da suke koyarwa a Makarantar, saboda yanda suka zama na kasa tsakanin Makarantarantun Kimiyya da ke kasar nan.

Da yake nashi jawabin, shugaban Makarantar Injiniya Muhammad kabir Abdullahi, godiya ya yi ga gwamnatin Jihar Kaduna saboda Wadata su da kudaden aikace-aikace da shi ne silar samun nasarar karbar bakin, har ma da aiwatar da wasu muhinman ayyukan cigaba a harabar Makarantar, kuma ya tabbatar da cewa shi da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin gudanarwa na aiki ba dare ba rana domin Cigaban Makarantar ta Nuhu Bamalli.

Daga karshe ya rufe da fatan samun amincewar hukumar ta NBTE a dukkanin kwasa-kwasan da tawagarsu suka duba yayin ziyarar tasu.

Karin Labarai

UA-131299779-2