Labarai

Gobara ta tashi a kasuwar garin Maradi na Jamhuriyar Nijar

Ibrahim Mustapha Maiduguri

Mummunar Gobara ta kama kasuwar Lafte dake jihar Maradin Jamhuriyar Nijar.

Da yake tabbatar da afkuwar gobarar, shugaban kasuwar, Sullemani Useni, ya shaidawa DABO FM cewar an samu asarar dukiyar miliyoyi a yayin gobarar.

Ya kuma bayyana cewar sun zargi wutar lantarki da haddasa gobarar.

Sai dai a cewar wasu masu kasuwanci a kasuwar sun bayyana cewar sun shafe kwanki biyu babu wutar lantarki a kasuwar kafin afkuwar gobarar.

A wani labari kuma, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana kasar Nijar a matsayin wadda bata daukar matakan kariya daga cutar Coronavirus.

DABO FM ta tattara cewar tini dai aka tabbatar da mutane kusan 400 da suka kamu da cutar Covid-19 a Jamhuriyar Nijar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano: Gobara ta tashi a kasuwar Sabon Gari

Dabo Online

Karon farko, an samu saukar dusar Kankara a gari mafi zafi na Jamhuriyar Nijar

Dabo Online

Daga kasar Nijar, wasu dalibai sun nuna murnar su ga nasarar Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu

#SunusiOscar442: Adam A. Zango ya fice daga Masana’antar Kannywood

Dabo Online

Gobara ta kone kamfanin giya a jihar Abia

Dabo Online
UA-131299779-2