Labarai

Yanzu-yanzu: Ganduje ya sanya dokar hana fita a Kano, masu Covid-19 a jihar sun zama 4

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje , ya sanya dokar hana fita a jihar Kano baki daya.

Gwamnan ya bayyana haka ne yau Talata a fadar gwamnatin jihar.

DABO FM ta tattara cewar Ganduje yace dokar zata fara aiki ne daga ranar Alhamis 16 ga watan Afrilu da misalin karfe 10, za kuma ta kasance mai wa’adin mako guda.

Haka zalika, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta tabbatar da samun karuwa wadanda suka kamu da cutar Kwabid-19 a jihar.

Ma’aikatar da bayyana haka ne a ingantaccen shafinta na Twitter a yau Talata.

“A daidai karfe 6:00 na yammacin yau 14 ga watan Afrilu, an tabbatar da samun karin mai dauke da Coronavirus.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Mutane 2 sun sake kamuwa da Covid-19 a Kano, jumilla 3

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu-yanzu: An kara tsawaita dokar kulle a Kano na tsawon sati 2

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 10 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 37

Dabo Online

An zargi wanda ya kamu da Kwabid-19 a Kano da shigar da cutar da ‘ganganci’

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2