Labarai

Gwamnan Adamawa ya bayar da sadakar albashinshi na watanni 3 domin yaki da Kwabid-19

Ibrahim Mustapha

Gwamnan jihar Adamawa, Rt Adamu Fintiri, ya bayar da sadakar albashinshi na watanni 3 domin taimakon jihar wajen yakar cutar Koronabairas a jihar.

Hakan na dauke a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ya fitar a ga manema labarai a yau Talata.

DABO FM ta tattara cewar gwamnan yace zai fara bayar da albashin daga watan Afrilu da ake ciki.

Ya kuma yi kira da dukkanin mutanen ciki da wajen jihar domin su baiwa gwamnatin tallafi wajen kawar da cutar daga cikin jihar.

Gwamnan yace; “Yanzu ne lokacin da yakamata muyi duk abinda yakamata ba sai mun jira cutar ta shigo mana sannan mu fara kokarin hana yaduwarta ba.”

Haka zalika gwamnan ya yaba wa babban malamin addinin Kiristanci, Rabaran Peter Makanto bisa bayar da gudunmawar asibiti mai gado 100 domin ya zama wajen killace za a samu da cutar.

Daga karshe yayi kira ga al’umma da su cigaba da kula da tsaftar jiki da ta muhalli domin yakar cutar a fadin jihar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Adamawa: Ni zan fara biyan albashin N30,000, dalibai zasuyi NECO da WAEC Kyauta – Fintiri

Dabo Online

Fintiri ya soke biyan kudin makaranta a Adamawa, ya dawo da shirin ciyarwa a Makarantu

Dabo Online

Adamawa: Fintiri ya kwace filayen makaratu da aka rabawa wasu shafaffu da mai

Dabo Online
UA-131299779-2