Gobe Asabar Mai Martaba Sarkin Zazzau zai cika shekaru 45 akan mulki

Mu’azu Abubakar Albarkawa

Zaria, Kaduna.

Yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin fara bukukuwan cikar Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Kaduna Alhaji Shehu Idris, shekaru 45 a karagar mulkin masarautar Zazzau.

A zagayen da Dabo FM ta yi, ya gano yadda al’umma a garin Zaria ke ci gaba da shirin gudanar da hawan daba a wani bangare na murnar wannan rana.

DABO FM ta tattara cewa Hakimai da masu rike da sarautun 44 ne za su yi hawan Daba.
Kuma ana sa ran halartan baki daga sassa daban-daban na ciki da wajen kasar nan.

Zuwa yanzu aikace-aikace sun yi nisa domin kawata fadar mai cike da dumbin tarihi.

Tuni dai aka ci gaba da shirya tarukan addu’oi da hawan dawakai har ma da maban-banta wasannin nishadantarwa a sassa daban-daban na masarautar.

Ko a Alhamis din da ta gabata, kungiyar’yan jaridu ta kasa ta kai ziyarar taya murna ga Sarkin a fadar sa, Kuma suka bayyana aniyar su na daukar shirye-shiryen da za’a gudanar a ranar Asabar 8 ga watan Fabrairun 2020.

A shekarar 1975, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, sai masu zaɓen sarkin Zazzau suka zaɓi Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr.) Shehu Idris a matsayin sabon sarkin Zazzau, zaɓen da ya samu amincewa daga gwamnatin jahar Tsakiyar Arewa wacce ke da helikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamna Manjo Abba Kyari.

Wannan naɗi nasa shi ya mai da shi sarkin Zazzau na 18 a jerin sarakunan Fulani, sannan kuma sarki na 3 a zuriyar Katsinawa.
Kuma shi ne sarki mafi dadewa a tarihin Zazzau.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.