Ziyarar godiya muka kai wa Buhari – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ziyarar da masu madafun ikon jihar Kano suka kai wa shugaba Buhari a matsayin ziyarar ‘godiya’.

A yau Juma’a ne dai gwamnan ya jagoranci shuwagabannin siyasa da na sarauta a jihar zuwa wajen shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, gwamna Ganduje yace ‘ziyarar godiya’ suka kai bisa ga yadda shugaba Buhari yake baiwa Kano goyon baya wajen ayyukan raya kasa da inganta tsaro.

Daga cikin yan tawagar sun hada da sanatoci da yan majalissun tarayya masu wakiltar al’ummar jihar Kano, Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Masu Alaƙa  Shugaba Buhari ya dauki hanyar zuwa kasar Jordan da Dubai

Sauran sun hada da mawaka irinsu Dauda Kahutu Rarara da sauran yan siyasar jihar da suka hada da sabbin wadanda sukayi kaura daga PDP zuwa APC irinsu Hajiya Binta Spikin.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.