Gobe Talata, ranar Sallar Idi karama – Sultan

Yau Litinin, 3 watan Yuli, 2019, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440.

Mai Alfarma Sarki Musulmi, Sultan Abubakar Sa’ad ne ya bayyana haka a fadarshi dake jihar Sokoto inda aka zauna domin karbar rahotannin ganin watan Shawwal daga sassan kasar Najeriya.

“Gobe Litinin, 1 ga watan Shawwal na shekarar 1440 bayan Hijirar Manzon Allah (S.A.W), wanda yayi dai dai da 4 ga watan Yulin 2019 (Miladiya)” – Sultan

“Mun samu labari da tabbacin ganin watan daga shuwagabanni addinin musulunci daban daban kamar su Shehun Borno, SARkin Gwandu, Sarkin Dutse, Sarkin Guru da kuma wasu wurare a nan jihar Sokoto.”


%d bloggers like this: