Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Hukumar yaki da Cin hanci ta jihar Kano ta bukaci a dakatar da Sarki Sunusi

2 min read

Hukumar karfe korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tayi kira ga zuwa dakatar da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, biyo bayan bannatar kudade tare da cewa ba’a kashe kudaden bisa ka’ida ba, wadanda suka kai Naira Biliyan 3.4

Hukumar tace an bannatar da kudaden tsakanin shekarar 2014 da 2017.

Majiyoyin DaboFM sun rawaito cewa hukumar ta fitar da bayanan ne a wani rahoto da kwamitin data nada na bincikar masarautar ya gudanar wanda shugaban Kwamitin, Muhuyi Magaji ya sanyawa hannu tare da mikawa manema labarai a ranar Litinin.

Rahotan yace, hukumar tayi bincike ne bisa karar da aka shigar gabanta na bannatar da kudade tare da yin abinda bashi da al’fanu da kudaden Masarautar Kano karkashin mulkin Sarki Muhammadu Sunusi II.

Binciken hukumar ya binciko cewa masarautar ta kashe sama da Naira 1.4 wajen kayayyaki data kira da bogi wadanda babu su da kuma rashin dacewar siyan wasu.

Bugu da kari, DaboFM ta binciko; Hukumar ta tuhumi masarautar da kashe da bannatar da sama da Naira biliyan 1.9 wajen siyan kayayyakin bukatun ta marasa amfani, wanda ya hada jimillar kudaden da ake zarginta da bannatarwa.

Hukumar tace, kayayyakin da masarautar da siya ya sabawa Sashi na 120 na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da Sashi na 8 na kudin dokar kashe kudaden Masarautar Kano na shekarar 1999.

Dadin dadawa, hukumar tace kayayyakin da masarautar ta siya ya sabawa Sashi 314 na kudin manyan laifuka da Sashi na 26 na Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano na shekarar 2008.

“Bisa ga shaidu dake gaban wannan hukuma, Sarki Muhammadu SUnusi II yaki bada hadin kai wajen gudanar da bincikenta bayan daya bawa dukkanin ma’aikatan masarautar kin amsa gayyatar da hukumar take aikewa wasu daga cikinsu.”

“Kin amsa gayyatar tasu yana hanamu cigaba da bincike, kuma yin hakan ya sabawa Sashi na 25 na dokar hukumar (2008)”

Hukumar ta bukaci da a dakatar da babban wanda ake tuhuma, Sarki Muhammadu SUnusi II tare da dukkanin wadanda ake tuhuma har sai an gama gudanar da bincike, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya, DaboFM da Daily Nigerian suka rawaito.

Hukumar ta kara kira da’a dakatar aikin da kamfanin Tri-C Nigeria Limited yakeyi na gyaran Ginin Babban Daki dake Kofar Kudu da Gidan Sarki dake Dorayi bisa kasancewar kamfanin na daya daga cikin wadanda ake zargi n, Alhaji Mannir Sunusi.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.