Labarai

Gwamna Zulum ya nada masu bashi shawara 27

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya nada nada masu bashi shawara na musamman guda 27.

A wata sanarwa da babban sakataren gwamnatin jihar, Hassan Mustapha Aminami ya bayyana sunayen wadanda gwamnan ya nada; Sheikh Muhammad Mustapha, Ali Audu Damasak, Mustapha Bulu, Hussaini Gambo, Bukar Busami Ardoram, Tukur Mshelia, Chief Kesta Ogualili, Muhammad Ibrahim Kwajaffa da Tijjani Modu.

Saura sun hada da Inna Galadima, Zahra Bukar, Mustapha Ali Sandabe, Gadau Ali Ngurno, Muhammad Maulud, Bole Modu Kachalla, Abdulrahman Albdulkarim, Bashir Maidugu, Bukar Modu Konduga, Umaru Saleh Gaya, Ali Zangeri, Tukur Ibrahim, Tijjani Lawan Kukawa, Abba Sadiq Gubio, Mallam Gana Badu, Yusuf Alao, Adamu Usman Chibok da Ahmad Asheikh Zarma.

Sanarwar tace za’a sanar dasu ranar da za’a rantsar dasu tare da rarraba bangarorinsu.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kayi addu’ar zaman lafiyar Borno yafi kayi tattakin zuwa waje na – Zullum ga mai tattaki

Dabo Online
UA-131299779-2