Home LabaraiBana bukatar sasantawa tsakani na da Buhari – Buba Galadima

Bana bukatar sasantawa tsakani na da Buhari – Buba Galadima

by Dabo Online
0 comments
Buba Galadima

Alhaji Buba Galadima, shugaban tsagin R-APC ya bayyana cewar baya bukaci sasantawa tsakaninshi da shugaba Muhammadu Buhari.

Da yake tattaunawa da jaridar Independent a ranar Laraba, Alhaji Buba Galadima yace babu matsala tsakaninsu balle ayi batun sasanci.

Buba Galadima ya kara da cewar tsakaninshi da shugaba Buhari babu takun sakar alkantaka duk da kuwa ya hana shi zuwa fadar gwamnatin Najeriya dake ‘Aso Rock’.

DABO FM ta tattara cewa Alhaji Buba Galadima yace yana taimakawa shugaba Buhari ne wajen gaya masa gaskiya komai dacinta wacce wadanda suke a kusa dashi basa iya fada masa..

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00