0
Gwamnan Bauchi, Dr Bala Muhammad ya tabbatar da nadin Balaraba Ibrahim a matsayin mai bashi shawara a kan walwalar mata zaurawa da ‘yammata marasa aure.
Rahoton DABO FM ya bayyana cewa takardar mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Muhammed Baba, tare da lambar GO/SS/POL/S/83, an rattaba mata hannu ne ranar 4 Augusta.
Kafin nadin nata, Malama Balaraba ita ce shigabar zawarawan jihar Bauchi baki daya.
