/

Ana zargin hadimin Ganduje, Alibaba da yin sama da fadin miliyan 16 na addu’ar Korona

Karatun minti 1

An zargi mai bawa gwamna, Abdullahi Umar Ganduje shawara akan harkar addinai, Alibaba Agama Lafiya Fagge da sama da fadin naira miliyan 16 hasafi ga malamai da sukayi addu’a a gidan gwamnati domin rokon Allah ya kawar da annobar Korona.

DABO FM ta tattara cewa a ranar 30 ga Yuli gwamnan kano, Abdullahi Ganduje ya gayyaci malamai 360 domin addu’ar Allah ya kawo karshen wannan annoba ta Kwaronabairos da ma rashin tsaron da ya addabi arewacin Najeriya.

Kwamishinan addinai, Baba Impossible ya tabbatar da Ganduje ya bayar da naira 50,000 ga kowanne malami da ya halarci addu’ar, ya kuma tabbatar da gwamna yayi jan kunnen kada wanda ya cire ko sisi daga abinda za’a bawa malamai 360.

Rohoton zargin ya bayyana Alibaba ya danne 45,000 daga kowanne malami wanda idan aka tattara kudin sun haura miliyan 16, daga karshe ya bisu da dubu biyar-biyar. Kamar yadda DailyIgerian ta fitar.

Cikin wani rahoto nagidan radiyon Freedom, Alibaba ya bayyana cewa “Kwarai dubu biyar-biyar muka bawa malaman da suka yi addu’a, sauran kudin kuma zamu karkasawa sauran malamai domin akwai wanda suka yi tasu addu’ar a gida da masallatai.”

Shugaban hukumar korafin cin hanci da rashawa na jihar Kano, Muhyi Magaji shima ya tabbatar da karbar korafin, kuma yayi alkawarin hukumar zata yi bincike tare da hukunta duk wani mai hannu a cikin wannan balahira.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog