Shin shugaban kasar Kamaru yana raye? – ‘Yan Kamaru mazauna Maiduguri sun nemi sanin gaskiyar lamari

Karatun minti 1

Wasu al ummar Kamaru dake zama a Maiduguri fadar Gwamnatin jihar Borno sunbayya cewa yanzu lokaci yayi da ya kamata a sanar dasu hakika nin gaskiya game da rashin ganin Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.

Wakilin Dabo FM a Maiduguri, Ibrahim Mustapha ya rawaito cewa ‘yan kasar Kamuru mazauna Maidugurin sun fadi hakane a wani taro da suka gudanar tare da takororin su na Najeriya, Nijar, da Chadi, a birnin Maiduguri.

Manufar taron dai shine inganta
yankunan kasashen, taron ya samu halartan manya daga gwamnatocin kasashen.

A cikin jawaban su, ‘yan kasar ta Kamaru sun bayyana cewa kusan sama da watanni 8 kenan babu labarin Paul Biya, a Talabijin ko a Radiyo.

Haka zalika sunkara dacewa ko aguguwar Korona Shugaban bai fito ya yiwa al’ummar kasar jawabi a fili ba kamar yadda sauran kasashe irin su Amurka, Saudiya, Najeriya, Nijer, suka yi ba.

Jaridar info-Cameroon ta rawaito cewa Paul Biya, baya raye kuma gawarsa tana Faransa, amma kuma fadar Gwamnatin kasar bata ce komai ba, haka zalika an rawaito cewa gidan Talabijin na mallakan Gwamnatin kasar bata dauko rahoton zaman aikin a ofishinsa sai dai a dinga ganin wakilai suna wakiltar sa, inda sukace a fada musu hakika nin lamarin su san masayinsu.

Kafafen yada labarai daga Kamaru sun sha yada labarai game da mutuwan Paul Biya, sai dai kuma fadar Gwamnatin kasar bata ce komai ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog