Home LabaraiYanzun nan: Soja ya kashe abokin aikinshi da farar hula mace daya a jihar Osun

Yanzun nan: Soja ya kashe abokin aikinshi da farar hula mace daya a jihar Osun

by Dabo Online
0 comments

Yanzunan, wani Soja mai suna Blessed Olodi na dake a sansanin sojoji na ‘Engineer Construction Regiment (ECT) a Ede, ya kashe abokin aikinshi da wata mata.

Daily Trust ta rawaito cewar majiyarta tace Sojan ya sokawa abokin aikin nashi wuta tare da wata mata da aka bayyana sunanta da Misis Iyabo. Ta kuma bayyana cewa tini dai aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo.

Mazauna unguwar Ede sun bayyana yacce Sojan ya takali fada tsakanin mutane 2 a ranar 2 ga watan Janairu, tare da cewa uwar gidanshi da wasu mutane hudu da wani kofura sun samu mummunan raunin yayin fadan.

Shaidun gani da ido sunje wadanda abin ya shafa sun samu mummunan rauni wanda yanzu haka suke shan magani a sashin kula da masu tsananin ciwo. Sun kuma bayyana yacce wasu sojoji suka karbe kayan da zai iya jiwa wani rauni na jikin sojan suka kuma tsare shi.

Daily Trust ta bincika cewar Sojan yana kan hutun neman lafiya daga inda yake aiki. Ta kuma tuntubi kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar, tace tana yin wani aiki, bata kuma ce komai ba bayan aike mata da sakon kar ta kwana.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00