Cristiano ya jefa kwallaye 3 rigis a wasanshi na farko a 2020

Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na kungiyar Juventus, ya jefa kwallaye 3 a wasan farko da ya buga a sabuwar shekar 2020.

Wasan gasar Serie A da kungiyar Juventus doke kungiyar Cagliari da ci 4 da nema a ranar Litinin, 6 ga watan Janairun 2020 a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Turin na kasar Itali.

DABO FM ta tattaro cewar Cristiano ya ne ya fara jefa kwallo a minti na 49 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A minti na 67, Ronaldo ya kara jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, mintuna na 81, dan wasa Gonzalo Higuain ya jefa ta 3.

Minti na 82, Ronaldo ya jefa kwallonshi ta 3 wanda ya kama Juventus ta jefa kwallo ta 4.

Masu Alaƙa  Kofin Zakaru: Bayan turnuku da gumurzu, Ronaldo ya fitar da Juventus kunya

Juventus tana kan mataki na 1 a teburin gasar Serie A ta kasar Italiya da maki 45 yayin da mai biye mata baya, Inter Millan, take da maki 42 da wasa daya a hannu.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.