Labarai

Da gaske Gwamnan jihar Ribas ya dakatar da Hukumar Alhazai ta jihar?

Kwanaki kadan bayan rushe zargin rushe Masallaci da ake yiwa gwamnan jihar Ribas, Nyseom Wike, ya sanar da dakatar da hukumar jin dadin Alhazai ta jihar.

Mataimakin Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, Alhaji
Abubakar Orlu, ya tabbatar da dakatar da hukumar har ma ya bayyana dalilin da yasa gwamnatin jihar tace ta rushe, kamar yacce Sahara Reporters ta tabbatar.

Shugaban ya bayyana cewa; Gwamnatin ta dakatar da hukumar ne bisa ayyukan rashin da’a hadi da cuwa-cuwar da tayi katutu tare da rashin hubbasa wajen gudanar da aikin hukumar bisa ka’ida.

Ya kara da cewa; a cikin hukumar, an samu dayawa ana karkatar da kujerun Hajji na jihar Ribas zuwa wasu jihohin.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani sakon manema labarai da ya fitar ranar Asabar.

Karin Labarai

Masu Alaka

N-Power: Gwamnatin tarayya ta dauki mutane 1,350 aiki a Ribas

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2