Nishadi

Ta tabbata: Jarumar Indiya ta watsa wa Ali Nuhu kasa a Ido bisa kin kulashi da tayi

Ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 2018, DABO FM ta fitar da wani rahoto kan cewa; Jaruma Shraddha Arya, ta kasar Indiya ta ki kula Sarki Ali Nuhu a lokacin da ya tayata murnar zagoyowar haihuwarta.

Hakan ya ja hankula kafofin yada labarai na harshen Hausa suka wallafa rahoto bayan samun gaskiyar al’amarin tare da yin rubutu da cewa “Jarumar ta wulakanta Ali Nuhu.”

Sai dai bayan yaduwar labarin, Jarumi Ali Nuhu ya shaidawa sashin Hausa na Legit.ng cewa; Labarin kanzon kurege ne kawai.

Hakan ya ja hankalinmu don sake yin rubutu tare da bayar da hujjojin rashin kulanshin da jarumar taki yi. (Dama DABO FM batace an wulakanta shi ba.)

  • Ga dukkanin ma’abota amfani da shafukan sada zumunta, sun san ana bada filin So (Like) da kuma bayyana ra’ayi (Comment) akan dukkanin wani rubutu ko hoto da aka wallafa.
  • A yanayi na zamanin yanzu, idan fitattun mutane suna murnar zagayowar haihuwa, abokai da yan uwa suna dora su a shafukansu na sadarwa domin taya murna. Suma a nasu bangaren wadanda ake yi wa murna da fatan alheri, sun bin shafukan wadanda sukayi musu murna domin suyi godiya da nuna jin dadi.
  • Duba da fitowar saka ‘Story’ a Instagram, wanda ka saka hotonshi na fatan alheri a ‘Story’ na shafinka, zai iya dorawa a kan nashi ‘Story’ dake shafinshi domin nuna godiya har na tsawon awanni 24.

Jarumi Ali Nuhu ya wallafa sakon taya murnarshi a shafinshi na Instagram ga Jaruma Shradha Arya ta kasar Indiya a ranar da take cika shekaru 31.

A jerin rubutun sama mai alamar tauraro, babu wanda Ali Nuhu ya samu daga jarumar sakamakon tayata murna da yayi.

Kalli wannan bidiyon domin ganin yacce jarumar bata kula jarumin ba;

Zaku ga bata yi martani ko like ba, duk da cewa kusan mutane 6026 suka so rubutun da Sarki Ali Nuhu ya yi.

Babu niyyar cin mutunci ko batanci akan wannan rubutun.

Masu Alaka

Jarumar Indiya ta ki kula Ali Nuhu bayan ya tayata murnar cika shekaru 31

Dabo Online

Ko dan darajar sunan Ali Nuhu dana sakawa ‘da na, bai kamata ya kaini Kotu ba – Zango

Dabo Online

Gobara a KANNYWOOD: Adam A. Zango ya zazzagi Ali Nuhu

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2