Labarai

Gwamnati na kashe N10,000 a duk gwaji 1 na gano Coronavirus – Minista

Dr Olurunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya na kasa yace gwamnati tarayya tana kashe N10,000 ko kusanta a yayin yin gwajin gano cutar Coronavirus duk guda 1.

Ministan yace tana amfani da Polymerase Chain Reaction (PCR), hanyar gwaji da kayan aikin da hukumar lafiya ta duniya ta sanya a matsayin mafi kyawun dake fitar da sakamakon cutar na kwarai.

Ministan ya bayyana haka ne yau a Abuja yayin da yake tattaunawa da manema labarai, kamar yadda The Sun ta rawaito.

Minsitan yace gwamnatin bata damuwa da kudaden da take kashewa illa iyaka tana da fatan gwajin ya rika fitar da sakamako na hakika wanda hakane dalilin da ya sanya ake amfani da Polymerase Chain Reaction (PCR) a Najeriya.

Yace Najeriya bata amfani da hanyar gwaji ta ‘Rapid Diagnostic Test (RDT)’ sakamakon rashin bayar da tabbacin inganci da hukumar WHO batayi ba.

“Bani da ainahi kudin amma anyi min nuni cewar kudin yakai N10,000 ko kusa da haka a duk gwajin da akeyi. Bani da wani tabbaci akan kudin.”

“Ko N10,000 ne, zaku adadin abinda za’a kashe duba da yadda ake tururuwa wajen yin gwajin.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu yanzu: An samu karin mutum 12 masu dauke da Coronavirus, jumilla 151 a Najeriya

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu-yanzu: Nasiru El Rufa’i ya kamu da Coronavirus

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 35 sun sake kamuwa da Koronabairas

Dangalan Muhammad Aliyu

Mutane 148 sun sake kamuwa da Kwabid-19, 32 a Kano, 14 a Zamfara da sauransu

Dabo Online

Buhari ya bada umarnin rabar da Shinkafar da Kwastam suka kama

Dabo Online

An samu mai Covid-19 na farko a Kano

Dabo Online
UA-131299779-2