0
Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 20 da daren yau Litinin.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 131.
“A daren yau da misalin karfe 9:00 an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 20.”
“An samu guda 13 a Legas, 4 a Abuja, 2 a Kaduna da guda 1 a jihar Oyo.”
Ga jerin adadin da aka tabbatar a kowacce jiha;
- Lagos – 81
- Abuja – 25
- Ogun – 3
- Inugu – 2
- Ekiti – 1
- Oyo – 8
- Edo – 2
- Bauchi – 2
- Osun – 2
- Rivers – 1
- Binuwai – 1
- Kaduna – 3
