Labarai

Gwamnati ta shirya tsaf domin fara karbar haraji daga hannun mutane milayan 45 -Shugaban Haraji

Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS), Babatunde Fowler, ya bayanna cewa nan da watan Disamba Najeriya za ta kammala tattara sunayen mutane miliyan 45 da za ta rika karbar haraji a hannun su.

Wakilin Dabo FM ya jiyo Mr Fowler a yau Alhamis a garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara yana bayanin a wurin kaddamar da Shirin Amfanin da Lambonin Tantance Masu Biyan Haraji (Tax Identification Number).

An fara kaddamar da shirin a Shiyyar Arewa ta Tsakiya, a Ilorin. A wurin, Fowler ya ce shekaru hudu na wannan gwamnatin a bada karfi sosai wajen inganta karfin tattalin arziki. Kuma wannan kokari ya na cimma ruwa a gimin da a ke yi.

“Farkon hawan wannan gwamnati, wadanda ake karbar haraji a wurin su ba su wuce mutane milyan 10 ba. Da tafiya ta mika, har ta kai mu na kadba ga mutane milyan 20.

“To a yanzu kuma shiri ya kammala yadda nan zuwa karshen watan Disamba za mu kai ga karin mutane milyan 25, sun zama milyan 45 kenan.”

Ya ce kowa zai samu lambar shaidar tantance cewa zai rika biyan haraji. Wannan lamba dai kamar lambar sa-idon gwamnati ce a kan asusun ajiya na bankuna, wato BVN.

Daga nan Fowler ya rika bada bayanin cewa irin nasarorin da ya samu wajen tara makudan kudaden harajin cikin gida, a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya nemi a samo hanyoyin kudaden shiga wadanda rika amfani da kudaden ana biyan karin albashin ma’aikata, wanda har yau maganar fara aiki da karin ta ki ci, ta ki cinyewa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Buhari zai ciwo bashin dalar Amurka miliyan 890 domin yaki da sauro

Muhammad Isma’il Makama

Ku haramta kungiyar Shi’a – Kotu ta umarci gwamnatin tarayya

Dabo Online

Next Level: Gwamnatin Tarayya ta aminta da fara aikin titin Jirgin Kasa na Ibadan-Kano

Dabo Online

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan ginin sabon filin tashin Jirage a jihar Ebonyi

Dangalan Muhammad Aliyu

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta bude iyakoki don cigaba da safarar motoci – Ali

Dabo Online
UA-131299779-2