Home LabaraiSai mun rage ma’aikata zamu iya biyan mafi karancin albashi – Ministan Kwadago

Sai mun rage ma’aikata zamu iya biyan mafi karancin albashi – Ministan Kwadago

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments
Chris Ngige

Ministan kwadago Mr Chris Ngige ya ce gwamnatin tarayya na jan kafar fara aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000 saboda sun duba sun ga abin da kamar wuya.

Jaridar The Nation ta ce ministan ya ce idan gwamnati ta fara biyan sabon albashin to za ta rinka kashe Naira Bilyan 580 a duk shekara. Abin da ya ce ba mai yiwuwa bane.

Mr. Ngige ya ce gwamnati na kauce wa zabin rage yawan maaikata kafin ta iya fara biyan sabon albashin don ta san hakan ba zai wa kowa dadi ba. Amma dai ya ce idan har kungiyar kwadugo ta dage akan wannan bukata to watakila sai sun rage ma’aikata.

Ministan ya fadi haka ne a ranar Alhamis lokacin da wakilan kungiyar kwadugo ta ULC suka kai masa ziyara.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00