//
Tuesday, April 7

Gwamnatin jihar Jigawa zata fara biyan albashin N30,000 a watan Disamba

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A wata sanarwa da mataimakin gwamna Badaru a sabbin kafafen yada labari na zamani, Auwalu D Sankara, ya saki ranar Laraba, ya bayyana kudurin gwamnatin na fara biyan albashin a wannan wata na Disamba.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar da kwamitocin bangarorin biyu suka cimma bayan watanni biyu ana tattaunawa.

Shima a nasa jawabin, gwamnan na jigawa yace biyan sabon albashin zai kara inganta tattalin arzikin jihar. Kuma an yi kokari wajen haduwa a tsakiya tsakanin bukatun ‘yan kwadagon da kuma ta gwamnati.

Idan dai za a iya tunawa, kimanin watanni biyu kenan da kafa kwamitin hadin gwiwar da zai duba aiwatar da tsarin biyan albashin. Wanda da yawa daga ma’aikatan jigawa hakan ya zo musu da mamaki, za a iya cewa gwamnan ya shammace su ne da batun biyan sabon maki karancin albashin.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020