Bincike

Ana ci gaba da samun Kamfanonin sarrafa Shinkafa ‘Yar gida bayan rufe iyakoki

Da yammacin yau wakilin Jaridar DaboFM na jihar Jigawa, Rilwanu Shehu ya ziyarci Kamfanin sarrafa Shinkafa na A. S. S. P VENTURES SARA dake karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Jaridar DaboFM ta samu zantawa da shugaban Kamfanin, Alh. Dankurgui Sara.

Ya shaida mana cewa kamfanin yana da tarin kayyakin aiki wanda da suka hada da; Injinan tace tsakuwa da kuma injinan wanke shinkafa ta fita Fes.

“Tabbas in da irin wadannan Kamfanoni to babu abin da zai hana Najeriya ta koma kamar sauran kasashen da suke tunkaho da noman Shinkafa”.

Shuganan kamfanin ya tabbatarwa da DABO FM cewa; suna karbar chasar Shinkafa daga mutane ko da kuwa buhu daya ne kacal a kudin da kowa zai iya biya.

Masu Alaka

Kungiyar masu sarrafa Shinkafa zasu fara siyar da kowanne buhu akan N13,300

Dabo Online
UA-131299779-2